Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta karyata labaran dake yawo a kafafen sada zumunta cewa ta bude wuraren rigistar katin zabe a kasashen waje.
Inda wani ya bayyana a kafar sada zumunta ta Facebook cewa hukumar ta bude wurare 21 a jamhuriyar Nijar.
Amma hukumar ta karyata hakan inda tace wannan magana ce wacce mai hankali ba amince da ita ba, kuma tana kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta dasu san irin labaran da zasu riga wallafa a shafikansu.