fbpx
Friday, July 1
Shadow

“Kanzan kuregene cewa mun share Peter Obi mun koma bayan Tinubu”>>Ohanaeze Ndigbo

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ta karyata rade raden da ake yi na cewa ta share dan takarar shugaban kasa na Labour Party ta koma bayan Tinubu.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Inyamuran  ta koma bayan Tinubu bayan da tsohon shugabata na jihar Legas yace tunda suna baya gwamna Sanwo Olu to zasu so dan takararsa na shugaban kasa.

Amma yanzu kungiyar ta fito ta karyata hakan tace tsohon shugaban mata na Legas bashi da hurumin da zai yi magana da yawunta, kuma bata koma Tinubu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.