Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ya baiwa matasan Najeriya shawarar cewa, kada su bar Najeriya a hannub masu lalatata.
Obasanjo yace lokaci yayi da matasan zasu tashi tsaye su yi aiki yanzu su daina yadda ana yaudararsu da cewa sune Shuwagabannin gobe.
Yayi wannan jawabinne a Abeokuta inda aka yi bikin cikarsa shekaru 85.
A matsayin shagalin wannan rana, an kuma raba kekenapep guda 85 ga mabukata.