fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Kar ku dagawa Osinbajo kafa idan kuka tashi tsige shugaba Buhari kan matsalar tsaro, Ohanaeze Ndigbo ta fadawa majalissaar tarayya

Kungiyar inyamuran Najeriya ta Ohanaeze Ndigbo ta cewa majalissar tarayya karta dagawa mataimakin shugaba Buhari kafa idan ta tashi tsige shugaban kasar akan mulki.

Inda kungiyar ta kara da cewa gabadayansu ne suka gaza ba shugaba Buhari kadai ba, saboda haka tare ya kamata su bar Villa.

Kuma tace tsige Buhari a dora Osinbajo na rikon kwarya kuskure ne domin bakan zai karawa dan takarar shugaban kasa na APC karfi, wato Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

A makon daya gabata ne majalissar ta bayyana cewa zata tsige shugaban kasar indan har bai magance matsalar tsaro ba nan da makonni shida.

Leave a Reply

Your email address will not be published.