Gaamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi masu motocin haya da masu Adaidaita Sahu da kada su sake su dauki wanda bai saka abin rufe hanci da baki ba a baben hawansu.
Gwamnan ya bayyana hakane a yayi da yake gabatarwa da kungiyoyi daban-daban abin rufe hanci da baki a gidan gwamnati a yau, Lahadi.
Yace ba zasu bari wasu su maida musu hannun Agogo baya ba bisa nasarar da suka samu a yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.
Yace ya baiwa jami’an tsaro umarnin kada su sassautawa duk wanda suka kama yana karya dokar Coronavirus/COVID-19.