Gwamnan jihar Rivers, Nyesom wanda ke neman takarar shugabancin Najeriya karkashin tutar PDP yayi kira ga shuwagabannin jam’iyyar cewa kar su sayarwa wanda zai tsere daga jam’iyyar bayan yaci zabe Fom.
Kuma gwamnan yasha alwashin kawo mutumin da zai maye gurbin Umahi a jihar Ebonyi, bayan shi Umahi ya koma jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakan ne a ziyarar daya kai jihar Ebonyi, inda yace shi ba zai taba barin PDP domin ta yi mai komai. Kuma yace idan har Umahi gwarzo yayi murabus ya sake neman wata kujera ya gani idan zai yi nasara.