fbpx
Monday, August 3
Shadow

Kar Ku Tsorata, Najeriya Ta Riga Ta Fara Biya Rancen Bashin Kasar China>>Amaechi

Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya ce Najeriya ta riga ta fara biya bashin China.
Amaechi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a wani shirin talabijin (Demokiradiyya Yau) da aka watsa a AIT ranar Asabar.
Majalisan wakilai ta kira Ameachi da wasu kan kwangilar layin dogo wanda kasar Sin ta bada dala miliyan 500 don ginawa.
Sin ta ba da rancen bashi ga Afirka
Ya ce, daga cikin dala miliyan 500 da gwamnatin tarayya ta dauka don gina layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna, an biya dala miliyan 96, ya kara da cewa Najeriya na da ikon biyan duk rancen Sin.
Muna biyan bashin.
“Najeriya ta rigaya ta fara biya sannan dala miliyan 500 ba mu muka karba ba, Shugaba Goodluck Jonathan ne ya karbi a lokacin mulkin shi kuma wannan magana tana nan,” in ji shi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *