Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci yan kasar cewa kar wanda ya zabi duk wani shugaban daya fada cewa matasa ne suka saya masa fom.
Yan siyasar da suka bayyana cewa matasa ne suka siya masu fom sun hada a Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Peter Obi da kuma Aminu Tambuwa duk a karkashin tutar PDP.
Inda yace duk makaryata ne saboda babu ta yadda matasa zasu hada masa naira miliyan 40 su siya masa fom din takara. Ya bayyana hakan ne a jihar Legas inda ya halacci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wani fasto.