fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kar ku zabi Tinubu domin zai haddasa yaki a Najeriya, cewar annabin Kiristoci

Annabin Kiristoci Joshua Iginla, yayi tsokaci kan tsayar da Musulmi da Musulmi da APC tayi a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa.

Joshua ya bayyana hakan ne a cocinsa dake babban birnin tarayya inda yace bai kamata APC tayi hakan ba domin Najeriya kasa ce mai addinai da yawa.

Saboda haka Tinubu zai haddasa yaki ne kawai a kasar idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa saboda abokin talarar shi Musulmi ne kamar shi.

A wannan watan ne Tinubu ya bayyana abokin takararsa bayan ya gana da shugana Buhari a Daura, inda ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Leave a Reply

Your email address will not be published.