fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Covid-19: “Kar kubude Makarantu da guraran kallan ball lokaci baiyi ba – Gwamnatin tarayya ta gargadi jahohin kasar

A ranar litinin gwamnatin tarayyar Najeriya ta aike da wani gargadi ga jahohin kasar kan kin bude makarantu guraran filin ball hadi da gidajan kallo.
Wannan gargadi na kunshe ne ta cikin bayanin da shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus kuma sakatare janar na shugaban kasa Boss Mustapha yayi a ranar litinin, a Abuja.
Kwamitin ya shawarci jahohi da su mutunta yar’jejeniyar haka zalika a cewar sa, “sam lokaci baiyi ba na bude makarantu da sauraran guraran dake tara cunkoson jama’a.
A satin da ya gabata gwamnatin jihar kano ta sanar da bude gidajan kallo, baya ga haka itama  jahar Cross River na shirin bude makarantun jahar dan cigaba da gudanar da karatu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.