Tsohon dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin ya shawarci ‘yan kudu masu gabashin Najeriya cewa su marawa Kwankwaso baya a shekarar 2023.
Inda yace idan suka zabi Kwankwaso to zai mika masu mulkin idan zamasa ya kare a matsayin shugaban kasa ya kare.
Amma yace kar su yaudari kanwunansu su fitar da dan takara a jam’iyyar Labour Party domin zasu yi asarar kuru’unsu kuma ba zasu yi nasara ba.
Ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels.