Wata karamar yarinya da aka boye sunanta ta bayyana yanda makwancinsu Rafiu Sanusi ya rika mata fyade har sau 5.
Yarinyar me shekaru 14 ta bayyana hakane ga kotun dake sauraren kararrakin cin zarafin mata dake Legas a yau, Talata.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya bayyana cewa, yarinyar na da shekaru 12 ne yayin da makwabcin nasu ya fara lalata da ita.
An daga ci gaba da sauraren karar zuwa 27 ga watan Yuni.
Karanta wannan Da Dumi Dumi: Shugaban karamar hukumar mahaifar Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar NNPP