Wani karamin yaro dan shekaru 18 a jihar Adamawa ya kashe wata mata ‘yar shekaru 36 da danta saboda ta ki yadda yayi lalata da ita.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Lamurde dake jihar.
Kakakin ‘yansandan jihar, Sulaiman Nguroje ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace an kama wanda ake zargi.
Yace matashin ya danna matar cikin ruwa wanda hakan yasa ta mutu, sai kuma shima danta me shekara 1 ya mai haka saida ya mutu.