fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Karancin man fetur zai iya haifar da tayar da kayar baya – NLC ta gayawa Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi gwamnatin tarayya cewa rashin karewa karanci da tsadar man fetur da ake fama da shi a fadin kasar na iya haifar da tayar da kayar baya.

Kungiyar ta NLC ta yi nuni da cewa karancin man dizal da na jiragen sama da ake fama da shi a halin yanzu ya fallasa gazawar da ake samu wajen dakile fasa kwabri da shigo da kayayyaki daga kasashen waje, wanda hakan na iya kawo matsala a harkar tsaro da zaman lafiya.

Karanta wannan  Yanzu-Yanzu Bola Tinubu na ganawa da Obasanjo a siriince

Kungiyar ta yi gargadin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa akwai iya adadin da jama’a za su iya jurewa wahalhalun da ake fuskanta a halin yanzu sakamakon karancin albarkatun man fetur, wanda idan jama’a suka kosa za su iya yin bori wanda hakan zai iya wargaza zaman lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.