Shafin yanar gizo na matambayi baya bata, watau Google, ya zama wata kafa da mutanen Duniya ke amfani da ita wajan neman amsar duk wani abu daya shige musu duhu, kusan ta kowane bangare, ilimi, addini, labarai dadai sauransu. Anan wasu bayanaine dangane da shafin na Google da zaka ji dadin saninu.
Kashi sha shida cikin dari na tambayoyin da akewa shafin google a kullun, bashi da amsarsu.
Kamin a canja mishi suna zuwa Google, ada sunan shafin Back rub.
A cikin ma’aikatan shafin na Google, akwai wadanda basu je makarantar jami’aba.
Idan ka rubuta kalmar “Askew” a cikin google, gaba dayan shafin zai karkace wa bangaren dama.
Idan ma’aikacin shafin google ya mutu, to abokin zamanshi(mata ko miji) za’a rika basu rabin albashin da mamacin ke dauka lokacin yana raye, har na tsawon shekaru goma, haka kuma idan yana da kananan ‘ya’ya za’arika biyansu kudi, dalar amurka dubu daya, kwatakwacin sama da naira, har sai
sun kai shekaru goma sha tara.
Shafin matambayi baya bata na Bing, yana biyan mutane dan suyi amfani dashi wajan neman bayanai maimakon suyi amfani da Google.
A duk minti daya, mutane na neman bayanai sau miliyan biyu a shafin google.
Shafin google ya doke na facebook a yawan mutanen dake amfani dashi: shine shafi na daya da mutane suka fi amfani dashi a Duniya.
A shekarar 2013 shafin Google ya samu tangarda, inda ya daina aiki na mintuna biyar, a wannan dan karamin lokacin, yawan mutanen dake shiga yanar gizo a Duniya, sun ragu da kashi arba’in cikin dari.
Kamfanin Google ya kirkiri wani kamfani me suna Caloci wanda wai zai rika maganin tsufa da kuma mutuwa.
Akwai wannan zanen tauraruwar ta yahudawa wadda akewa lakabi da “Star of David” a saman ginin filin jirgin saman kasar Iran, sama da shekaru talatin da suka gabata, ba’a san da itaba saida shafin google, ta hanyar manhajarnan ta “Google Map”, dake nuna gurare, suka hangota.
Da manhajarnan ta “Google Map” zaka iya ganin karkashin ruwa da halittun dake ciki.
Wadanda suka kirkiri shafin google, garejin motar wata mata suka kama haya suka fara amfani dashi, itama matar me suna Larry Page, yanzu, itace shugabar shafin Youtube.
Duk wani abu daka taba dubawa ko ka taba amfani da shafin google ka nema, sunada tarihinshi a gurinsu.