fbpx
Monday, October 26
Shadow

Karanta kaji amsar da Pep Guardiola ya bayar akan komawar Messi Premier League

Lionel Messi ya gigiza duniyar wasan kwallon kafa bayan da ya bukaci barin kungiyar Barcelona, kuma Manchester City itace kungiyar da ake sa ran dan wasan zai koma amma daga baya Messi ya tabbatar da zaman shi a Barcelona bayan yaki kai kungiyar kotu akan yarjejeniyar kwantirakin shi.

Manema labarai sun tambaya Pep Guardiola cewa shin wane dalili ne yasa City bata siya Messi ba, kuma zata siye a kaka mai zuwa?.  Sai kocin yace ba sai ya fadi komai ba akan hakan saboda Messi ya rigada yayi cikakkun bayanai akan wannan lamarin kuma shi dan wasan Barcelona ne wacce ta kasance kungiyar da yake so.
Pep Guardiola ya kara da cewa shi bai san ko Messi zai koma Manchester City ba a kaka mai zuwa kuma wannan tambayar ta Messi ce saboda shi bai san ra’ayin wasu mutune ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *