fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Karanta martanin da bankin Union ya mayarwa da wani me hulda dashi da ya ce ya barsu saboda suna so su saka rayiwarshi cikin tagayyara: Abin zai kayatar dakai

Watakan abin magana baya karewa, wannan labarin wani me ajiyar kudi dane da bankin Union wanda ya aikawa bankin da sako ta dandalinsu na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter cewa shifa daga yau ya daina hulda dasu domin ya lura cewa zasu tagayyarashi, irin martanin da suka bashi ya dauki hankulan mutane sosai ta yanda aka yita nanata batun da danna alamar son dakon.

Mutumin dai ya rubuta sakon nashi kamar haka ” Ina so in sanar daku cewa daga yau bazan kara ajiyar kudina daku ba har abada tunda naga alama kuna nema ku tagayyaramin da rayuwa, ina muku fatan Alheri”.

Koda bankin suka ga wannan sako sai suka mayarmishi da amsa kamar haka “Gebriel Temitope(sunan shikenan) muna so mu sanar dakai cewa muna matukar sonyin hulda dakai/muna ganin kimar ka bazamu taba saka rayuwarka cikin tagayyaraba. Duk wata dangantaka/hulda/ mu’a mulla da zakayi da wani, wataran sai an samu sabani(za mu zauna zomu saba) idan ana tare zama na soyayyar gaskiya ba kowa sai ya samu abinda yake soba dole kuyi hakuri da halayen juna, kazo muyi magana a asirce, gaba da gaba, mutum da banki”.

Karanta wannan  Mun nunawa Abba Gida-Gida Soyayya amma ya nuna mana kiyayya>>Inji Wani da aka rushewa shago a Kano

Wannan martani da bankin ya mayarwa da wannan mutumi ya matukar dauki hankulan mutane sosai, koda yake ga wadanda suka san wanene ke kula da dandalin sada zumu tar na bankin Union abin baizo musu da bazata ba, dama sun san a rina, dan kuwa sanannen tsohon me kula da dandalin sada zumunta na hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasane watau Olufemi Olukayode, wanda aka sanshi da iya magana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *