A yaune, korarriyar fitacciyar, jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ke murnar zagayowar ranar haihuwarta, ‘yan uwa, abokai da mutanen arziki suna ta tayata murna, fitaccen mawakinnan Classiq, wanda dalilin wakar da sukayi tarene aka koreta daga masana’antar fina-finan Hausa, shima ba’a barshi a bayaba, ya tayata murna.
Ga sakon da ya rubuta akan wannan muhimmiyar rana gurin Rahama Sadau.
“Hmmmm idan aka taso da batunki, ina da abubuwa da yawa dazan fada akanki, banma san ta inda zan fara ba, ke ta musamman ce, ina tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki, zababbiya, ki ji dadin wanan rana/ki more”