(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Shi kuma sai ya wallafa wannan sako na dan uwan nashi a dandalinshi na Twitter inda ya rubuta cewa dan uwanshi yana bukatar mata, wadda ta kammala karatun digiri kuma ta kasance tana da shekaru 24 zuwa 26, kuma ya kasance tana motsa jiki kuma ta iya girki sosai,Sannan yayan nashi yana daukar albashi sama da naira dubu dari biyu a wata.
Aikuwa sai aka samu wata ta aikamai da sakon sirri inda ta tambayeshi ko da gaske yake maganar da yayi, ya bayyana mata cewa da gaske yake, daga nan magana tayi karfi. Yanzu dai watan gobene auren yayan nashi idan Allah ya kaimu. Kuma sune a wadannan hotunan nasu na kamin biki.
Muna musu fatan Alheri da kuma Allah yasa ayi lafiya. Tun bayan daya wallafa wannan labari nashi sai abin ya kayatar da mutane akata sanya alheri da kuma nuna alamar jin dadin wannan labari.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});