fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Karanta yawan kudin da kasashen da suka yi nasarar zuwa gasar cin kofin Duniya zasu samu

Ko ka san nawane kowace kasar data kai gasar cin kofin Duniya zata samu, ga bayanan kudin da za’a baiwa kowacce kasa, kamar yanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito. Samun nasarar kaiwa mataki na gaba na karawa kasa yawan kudin da zata samu.

Kasashe talatin da biyune zasu buga gasar cin kofin Duniyar kuma an rarrabasu zuwa rukunai takwas, wanda kowane rukuni na dauke da kasashe hudu. a cikin kowane rukuni, kasashe biyune zasu fito, watau kasashe goma sha shida zasu fito, sha shida kuma, da aka fitar dasu, su koma gida.

Kasashe shadida da sukayi rashin nasara, za’a baiwa kowanensu kudi, dalar Amurka miliyan takwas, kwatankwacin sama da naira biliyan biyu.
Kasashe shashida kuma da sukayi nasara, suka kai mataki na gaba, za’a ba kowacensu kudi, dalar Amurka milyan sha biyu, kwatan kwacin sama da naira biliyan hudu.
Kasashen da suka kai wasan kusa dana kusa dana karshe kuwa za’a baiwa kowanensu kudi, dalar Amurka miliyan sha shida, kwatankwacin sama da naira biliyan biyar.
Kasar data kai matsayi na hudu kuwa, za’a bata kudi, dalar Amurka miliyan ashirin da biyu, kwatankwacin sama da naira biliyan bakwai.
Kasar data kai matsayi na uku kuwa za’a bata kudi, dalar amurka miliyan ashirin da hudu, kwatankwacin sama da naira biliyan takwas.
Kasar data kai matsayi na biyu kuwa, zata samu kudi, dalar Amurka miliyan ashirin da takwas, kwatankwacin sama da naira biliyan goma.
Sai kasar da tayi nasarar cin kofin Duniyar, za’a bata kudi, dalar Amurka miliyan talatin da takwas, kwantankwacin sama naira biliyan goma sha’uku.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *