Kwamishinan ‘yan sand na jihar Zamfara, Ayuba Elkana ya bayyana cewa har yanzu basu janye dokarsu ta haramrawa mutane mallakar makamai ba.
Inda yace hukumar ta daina ba mutanen dake son sayen bindiga lasisi. Kwamishinan ya bayyana hakan ne ranar lahadi bayan gwamna Matawalle yace su ba mutanen da suka cancanta lasisin mallakar bindigu don kare kanwunan su.
A ranar lahadin ne gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya umurci huukumar ‘yan sanda ta jihar cewa ta ba mutane damar mallakar bindugu don kare kawunansu.
Amma hukumar ta mayar masa da amsa cewa ba zata baiwa mutane lasisin mallakar bindugu ba domin hakan ya sabawa doka.