fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Kare na samun kulawar da mutane basa samu

A kasar Amurka, karnuka na samun irin kulawar da wasu mutanen basa samunta, anyi kiyasin cewa a shekarar data gabata, masu son da kiwon dabbobin gida, irin su mage da kare dadai sauransu sun kashe zunzurutun kudi dalar Amurka biliyan shida wajen kula dasu.

 Akwai guraren da ake kai karnukan dansu shakata, kuma a kula dasu yanda ya kamata, akwai wani hotal din karnukan da ake kai kare dan gata ya kwana cikin annashuwa, za’amai yankan farcensi, a gogesu a sakamusu wani mai da zaisa su rika sheki, akwai gurin ninkaya/wanka na musamman a gurin, haka kuma ana wankemusu  hakoransu, a musu tausa.

Idan aka kai kare daki, ya kasa yin barci, akwai ma’aikacin hotal din da aka ware na musamman da zai je ya debemishi kewa har ya kamu da barci ko kumama sai gari ya waye, haka kuma akwai gurare da aka ware dan motsa jikin karnukan, duk wadannan ayyuka da akewa karnukan biya mesu zaiyi, kudin suna farawa daga dala hamsin, dari, dari biyu, dari biyar, dubu daya, harma sama da haka, ya danganta da irin kulawar da mutum yakeso a baiwa karennashi. Lallali wannan shine Allah daya gari banban.

Karanta wannan  Yajin aikin ASUU ya kai kwanaki 140 ana yi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.