fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Karim Banzema ya bayyana cewa yana son yin ritaya a Lyon

Tauraron Real Madrid Karim Banzema ya bayyana cewa a kungiyar Lyon yake so yayi ritaya amma yanzu bai shirya komawa kungiyar ba.

 

 

Banzema ya shiga kungiyar madrida ne a shekara ta 2009 daga kungiyar Lyon a farashin euros miliyan 35 kuma yaci kwallaye har guda 241 a wasanni guda 501 daya buga a kulob din Real Madrid.
A watannin da suka gabata an samu labari cewa dan wasan mai shekaru 32 ya yarda zai kara tsawon kwangilar shi a kungiyar madrid har izuwa watan yuni na shekara ta 2022 duk da cewa har yanzu ba’a tabbatar da maganar ba.
Banzema baya tantama akan komawar shi Lyon koda kuwa ba’a matsayin dan wasa ba.
A ganawar da Banzema yayi da tashar yan wasan kwallon kafa na kasar faransa yace mutane sun san dangantakar shi da Lyon saboda haka babu abun da zai hana shi komawa Lyon koda kuwa ba’a matsayin dan wasa ba. Amma ba zai yiwu ya koma Lyon a yanzu ba saboda yana cikin babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya.
An tambaya Banzema cewa su waye manyan yan wasan da yayi aiki tare da su?. Sai yace manyan yan wasan da yayi aiki dasu suna da yawa, A kasar faransa yace akwai juninho [pernambucano] da [Sylvain] Wiltord, A kungiyar madrid kuma yayi aiki da Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos da dai sauran su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Leave a Reply

Your email address will not be published.