fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Karin hotunan yanda gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya raba tallafin kayan shayi: Wani yace gwamnan yana cin abinci da hannun hagu

A makon daya gabatane gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya raba kayan tallafin yin shayi ga mutane da dama a jihar, abin da ya dauki hankulan mutane sosai a kasarnan, anan wasu karin hotunan yanda abin ya wakanane.

Me kula da shafin sada zumunta da muhawara na gwamnatin jihar Kanon ne ya saka hotunan, hankalin wani bawan Allah yakai kan wani hoto da gwamnan ya amshi biredi da hannun hagu, sai yace “ya sha shayi ya more amma ya daina cin abu da hannun hagu”.

Me kula da shafin na sada zumunta na jihar Kanon ya tambayi mutumin cewa ina yaga gwamnan yaci abinci da hanun hagu? ya dauka da hannun hagu dai amma be kai bakinshi ba.

Daga nan sai mutumin ya saki kari.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *