fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Karin kudin Man Fetur: Yajin aiki ba gudu ba ja da baya>>NLC

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta bayyana cewa yajin aiki akan karin kudin mai dana Wutar Lantarki ba gudu ba ja da baya.

 

NLC ta bayyana hakane ta bakin shugabanta, Ayuba Wabba bayan zaman ganawa na masu ruwa da tsaki na kungiyar a Abuja.

Ya bayyana cewa shi da wakilan kungiyar daga sauran jihohin Najeriya sun yanke shawarar zasu ci gaba da aniyarsu ta yin yajin aiki da zanga-zanga daga ranar 28 ga watan Satuma, watau ranar Litinin me zuwa kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.