fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Karku sake inji kuna amfani da matsayinku wajan baiwa ‘yan uwanku aikin Gwamnati>>Shugaba Buhari ya gargadi Hadimansa

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya gargadi jami’an gwamnatinsa da cewa kar su sake su rika amfani da matsayin da suke dashi wajan baiwa na kusa dasu taimakon da baya kan doka, musamman wajan samun aikin gwamnati.

 

Shugaban ya bayyana hakane ta bakin Ministan labarai,  Lai Muhammad inda yace irin hakan ba tsarin da gwamnatinsa ta dauko ba kenan.

Yace wannan kira ya zama wajibu saboda yanda wasu ke amfani da takardu ko kuma shaida daga wasu manyan jami’an gwamnati suna neman aiki a wasu ma’aikatu.

Karanta wannan  Gwamna El Rufa'i yayi fashin baki kan sauyawa jihar Kaduna suna

 

Yace an baiwa duka ma’aikatun gwamnati umarnin kada su saurari duk wani da zai je musu da wata takarda ko kuma shaidar cewa wani babban jami’an gwamnatine ya aikoshi a bashi aiki. Yace an samar da tsarin da za’a wa kowa adalci wajan neman aiki ko kwangila a gwamnatinsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.