fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

KAROTA ta kama maganin Karfin maza na Naira Miliyan 25

Hukumar dake kula da bin dokar tuki a Kano,KAROTA ta kama maganin karfin kuzarin maza da darajarsa ta kai ta Naira Miliyan 25.

 

An kama maganinne a Sabon Gari, sunan Maganin Arofranil, kamen ya tabbata ne bayan da aka kyankyasawa KAROTA cewa maganin bashi da rijistar NAFDAC.

Katan Dubu 5 na maganinne aka kama yayin da yake cike a cikin wata mota ana shirin fara rabonsa. Saidai ba’a samu nasarar kama masu maganin ba.

 

Shugaban hukumar KAROTA, Dr. Baffa Dan Agundi yayi kira ga jama’a dasu ci gaba da basu hadin kai dan aikinsu ya rika tafiya daidai. Za’a mikawa hukumar Lafiya ta jihar maganin dan ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published.