Hukumar Kwastam ta bayyana cewa basa sayar da shinkafar da suka kwace daga hannun ‘yan kasuwa.
Tace duk rade radin da ake akan hakan ba gaskiya bane.
Tace idan shinkafar da suka kwace me kyauce, zasu baiwa ‘yan gudun hijira, idan kuma ba mai kyau bace, to zasu baiwa masu gidajen kaji.
Daya daga cikin kwamandan Kwastam, Dera Nnadi ne ya bayyana haka.