Kungiyar dake ikirarin kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa, bata ce bata tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba.
Ta bayyana hakane ta bakin sakatarenta Chiedozie Ogbonnia inda tace labaran da ake yadawa akanta ba gaskiya bane.
Tace tabbas tana sin Inyamuri ya zama shugaban kasa amma dai har yanzu bata fitar da matsayinta ba kan wanda zata goyawa baya ba.