Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, bai ce APC ta fitar da dan takara ba tare da yin zaben fidda gwani ba.
Bayan ganawarsa ds gwamnonin APC kamin ya wuce kasar Sifaniya, an samu Rahotannin dake cewa, shugaban kasar ya nemi a zabi dan takara na bai daya ba tade da zabeba.
Rahotonni sun nuna cewa tuni ma har an samu wasu gwamnonin jam’iyyar sun fara zama dan fitar da dan takara guda daya kamar yanda shugaban kasar ya bukata.
Saidai a ta bakin kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, yace wannan magana ba gaskiya bace, shugaban kasar bai gayawa gwamnonin haka ba.