fbpx
Monday, August 15
Shadow

Karya ake min ban gana da Wike a kasar Faransa ba, amma kofa a bude take, cewar Bola Ahmad Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana cewa karya ake make masa bai gana da gwamnan Rivers Wike ba a kasar Faransa.

Amma ya kara da cewa kof a hude take ga duk wani babban mutumin dake son ganawa dashi, amma dai a halin yanzu bai gana da Nyesom Wike ba.

Mai ba gwamnan Legas shawara ne ya wallafa wannan labarin duk da dai ya goge shi amma hakan ya tayar da zaune tsaye a jam’iyyar PDP.

Domin ta fara tunanin watakila Wike zai koma APC biyo bayan har yanzu bai huce ba da abinda Atiku yayi masa na kin zabar shi a matsayin abokin takara ba duk da yayi masa alkawari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.