fbpx
Monday, August 15
Shadow

Karya ake min ban kaddamar da Tinubu ba domin ko a zaben fidda gwani ban janye masa ba, cewar Fasto Bakare

Tsohon dan takarar shugaban kasa na APC wanda ya fafi zaben fidda gwani, Fasto Tunde Bakare yace shi bai kaddamar da Tinubu ba.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan rahotannin dake bayyana cewa ya juyawa kungiyar Kirista ta CAN baya a matsayinsa na Fasto ya kaddamar da Musulmai.

Amma ya fito fito ya karyata hakan inda yace shi bai kaddamar da Tinubu da Kashim Shettima ba kazafi ake masa.

A karshe yace ta yaya zai kaddamar da mutumin da ko a zaben fidda gwani bai janye masa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.