Gwamnan jihar Rivers kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Nyesom Wike ya bayyana cewa Atiku Abubakar karya yeke yi daya ce ya nemi sulhu a wurinsa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yau ranar juma’a yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels bayan ya dawo daga kasar Sifaniya.
Wike da Atiku sun nemi tikitin shugaba kasa na jam’iyyar amma Atiku ya doke shi wanda hakan yasa ya fusata, sannan kuma Atiku ya tsallake shi ya zabi Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.
Wannan dalilin ne yasa har yanzu basa jituwa, amma Atiku yace ya nemi sulhu, sai da fa Wike yace karya yake bai nemi sulhu ba hasali ko aike bai yi masa ba tun bayan zaben fidda gwani a watan Mayu.