Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ken Nnamani, ya bayyana yadda ake cewa wasu kungiyoyin suna sayen fom din tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar ga wasu ‘yan takara a matsayin “babban karya”.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise TV a yau 12 ga Mayu, Nnamani ya ce ikirari na cewa kungiyoyin tallafi da dama sun siya fom ga dan takarar da suka fi so duk karya ne saboda wa su daga cikin su ba su da kudin da za su biya hayar gidajen da suke zama. Ya ce dole ne a dakatar da lamarin nan take.