fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Karyane bama muzgunawa Kiristoci a Najeriya>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da kiran da wasu sanatocin kasar Amurka suka yi na sake saka Najariya a cikin kasashen dake muzgunawa Kiristoci.

 

Sanatocin sun aikewa shugaban kasar ta Amurka da bukatar inda suke zargin cewa wai ba’a barin kiristoci na yin addininsu yanda ya kamata a Najeriya.

 

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa, wannan magana an yi tane akan karya da kuma rashin fahimtar abinda ke faruwa a Najeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran Najariya, NAN, ya ruwaito Lai Muhammad yana kasar Ingila ne dan ganawa kafafen sadarwa na kasa da kasa da kuma sauran kungiyoyi masu zaman kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.