fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Karyane labarin wai daya daga cikin likitocin kasar China da suka zo Najeriya ya kamu da Coronavirus/COVID-19>>Gwamnatin Tarayya

Ministan watsa labarai da Al’adu,Alhaji Lai Muhammad ya karyata cewa ana rabawa kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 Miliyan 700.

 

Lai Muhammad ya kuma karyata labaran dake yawo cewa wai daya daga cikin likitocin kasar Chinarnan da suka zo Najeriya kuma yanzu haka suke killace ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Lai yace labaran basu da tushe balle makama, yayi kira da mutane su daina bin labarin da ba daga hukumar NCDC ya fito ba da wanda kuma ba daga kwamitin shugaban kasar ya fito ba.

Karanta wannan  Yanzu-Yanzu Bola Tinubu na ganawa da Obasanjo a siriince

 

Lai Muhammad ya bayyana hakane a ganawar da kwamitin shugaban kasar yayi da manema labari a Ranar Laraba kamar yanda suka saba kullun-kullun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.