Sunday, June 7
Shadow

‘Kasancewar Amurka ja gaba a yawan masu korona daukaka ce’A>>Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce kasancewar Amurka a gaba wajen yawan masu cutar korona “alamar girma”.

Shugaban ya ce “ina kallon wannan abu a matsayin wani abun alkairi saboda hakan na nufin mun fi kowa yin sahihin gwajin cutar.”

Amurka na da mutum miliyan 1.5 da ke dauke da cutar ta korona inda kimanin 92,000 suka mutu, kamar yadda jami’ar Johns Hopkins University ta rawaito.

Kasar Russia ce dai ke biye wa Amurkar inda take da mutum kimanin 300,000 masu dauke da cutar.

Shugaba Trump dai ya bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya wa’adin kwana 30 da ko dai ta fito da mafita kan cutar ko kuma Amurka ta fita fit daga hukumar abin da ke nuni da irin biliyoyin dalolon da hukumar ka iya rasawa.

Har wa yau, Shugaba Trump ya ayyana maganin maleriya na hydroxychloroquine a mastayin maganin korona.

Sai dai masana da likitoci sun soki wannan ikrarin nasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *