Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewa baya tsoron mayan yan siyasar dake neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC.
Inda yace yanada yakinin cewa duk zai doke su kuma shi jam’iyyar APC zata tsayar a matsayin dan takararta a shekarar 2023.
A karshe ya kara da cewa kasancewar Tinubu daya gada cikin mutanen da suka kirkiri jam’iyyar APC ba zai sa a bashi tikiti ba, saboda haka ba zai yi kasa a gwiwa ba.