Kasar Amurka tace ‘yan kasarta matasa kadanne suka cancanci shiga aikin soja kuma a cikin kadandin, da yawa basa son aikin.
Sanarwar tace yawanci abinda ke hana matasan shiga aikin sojan shine tsoron samun rauni, mutuwa da tabuwar kwakwalwa.
Hukumar sojojin ta koka da wannan lamari inda tace yana ci mata tuwo a kwarya, karin abinda ke sa ana samun karancin masu shiga aikin sojan a kasar Amurka shine dokokin dake tattare da daukar aikin.