Kasar Amurka ta amince ta sayarwa da Najeriya makamai da suka hada da jiragen sama na musamman akan kudi kusan dala biliyan $1.
A baya dai kasar Amurka ta ki amincewa ta sayarwa da Najeriya makaman saboda zargin take hakkin bil’adama.
Saidai a yanzu saboda tsanantar matsalar tsaro, kasar ta amince ta kerawa Najeriya makaman.
Jirgi na musamman da za’a kerawa Najeriya sunansa 12 AH-1Z wanda aikinshi shine yaki da ‘yan ta’adda.
Majalisar kasar Amurka ta amince a kerawa Najeriya makaman.