fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Kasar Amurka ta yi gargadin kungiyoyin ‘yan ta’adda na ISWAP da Al-Qaeda na mamaya a Africa

Kasar Amurka ta bayyana cewa sai kasashen Africa sun dage da kuma kula da yanda zasu yi maganin ‘yan ta’adda saboda manyan kungiyoyin ‘yan ta’adda na Duniya, ISIS da Al-Qaeda na kwarara cikin yankin Africa ta yamma.

 

Wani janar din kasar Amurka dake kula da yanayin tsaron Africa, Janar Davin Anderson ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai.

Yace kungiyoyin sun shiga kasashen Mali da Burkina Faso suna mamaye gurare tare da karbar haraji.

 

Yace bayan yin galaba akansu a kasashen Syria da Iraqi, sun zabi shiga kasashen Africa saidai basa bayyana kansu, suna ayyukansu ne a boye.

Leave a Reply

Your email address will not be published.