fbpx
Monday, December 5
Shadow

Kasar Amurka zata kakabawa duk wanda aka kama da hannu a kisan musulmin kasar Myanmar/Burma

Secretary of State Rex Tillerson is pictured. | AP
A ziyarar kwana daya da ya kai kasar Myanmar, bayan samun rahotanni masu tayar da hankali akan kisan da sojoji har dama mutanen gari kewa kabilar musulmi ta Rohingya a kasar ta Myanmar, Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson a wani taron da yayi da shugabar kasar Aung San Suu kyi ya bayyana cewa kasar Amurkar ta matukar damu da irin rahotannin cin zarafin da ake samu sojoji na yiwa musulman kasar wanda yayi sanadiyyar tserewar da yawa zuwa makwabciyar kasar Bangladesh dan yin gudun hijira, kuma suna so ayi bincike me zaman kanshi akan wannan lamari.

Tillerson ya kara da cewa duk wanda aka samu da hannu a wannan rikici to zasu kakaba mai takunkumi amma ba zasu sakawa gaba dayan kasar takunkumin karya tattalin arziki ba. 
Shugabar kasar wadda a kundin tsarin mulkin kasar bata da iko da yankin da sojojin ke cin zarafin, an zargeta da kin yin Allah wadai da wannan cin zarafi da akewa musulmi, amma ta fito ta kare kanta inda tace tafa yi magana amma watakila mutane basu gamsu da abinda ta fada bane shiyasa ake surutai.
A wani rahoto da wata kungiyar kasar Amurka me suna Fortify Right ta rubuta tace ta samu labaran kisan kare dangin da sojoji harma da mutanen gari ke yiwa musulmai a kasar ta Myanmar da kona su da ransu da yiwa kananan yara fyade  da sauran munanan abubuwa, shugaban kungiyar yace wannan abu ya wuce ace wai ayi Allah wadai dashi kamata yayi kungiyoyin kasa da kasa su dauki mataki na zahiri in kuwa ba haka ba to za’a ci gaba da wannan abu.
Amma sojojin kasar sun karyata wannan rahoto inda sukace sun fadane kawai da wasu ‘yan kungiyar tada kayar baya a yankin.
Mun fatan Allah ya kaiwa Musulman Rohingya dauki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Kalli Bidiyo: Shi Ma Fa Aminu Ya Ci Kudin Talakawa Domin An Dana Shi A Jirgin Gwamnati

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *