fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Kasar China na son sace bayanan binciken da muke na nemo maganin cutar Coronavirus >>Inji Kasar Amurka

Kasar Amurka ta zargi kasar China da mata kutse dan satar bayanan binciken da take na gano maganin cutar Coronavirus.

 

Manyan hukumomin bincike da leken Asiri na kasar Amurka, FBI da CISA suka bayyana haka a bayanan da suka fitar kwanakwanannan.

 

Har yanzu dai babu magani ko rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 da aka samar kuma duk kasar data samar dashi to ta ciri tuta sannan zata samu makudan kudin shiga.

 

A ganawar da yayi da manema labarai  Ranar Litinin,Shugaban Amurka ya amsa tambaya kan satar bayanan da kasar China take yunkurin yi musu inda ya bayyana cewa ai indai China ce zata iyayin komai, ba sabon abu bane, ya kara da cewa baya farin ciki da kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.