Indiya ta bayyana shirinta na zurfafa alakar tattalin arziki da Najeriya don bunkasa saka jari da kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Amb Abhay Thakur, babban kwamishiann kasar shine ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kaiwa Gwamna Abdullahi Ganduje a ranar Juma’a a Kano.
Thakur ya bayyana cewa akwai da dadaddiyar dangantaka da girmama juna tsakanin kasashan biyu, wanda ya samu asali tun bayan samun ‘yancin kan kasashen.
A cewarsa, Najeriya ita ce babbar abokiyar kasuwancin kasar Indiya a Afurka.
A karshe Thakur ya yi kira tare da bukatar karin hadin gwiwar cinikayya tsakanin Najeriya da Indiya a matsayin wata hanya ta bunkasa dangantaka da huldar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.
A nasa jawabin Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatarwa kwamishinan cewa Dangantar Najeriya da kasar indiya zata cigaba da dorewa.