Damisar da aka sauya wa matsuguni daga Namibiya zuwa Indiya a shekarar da ta gabata, ta haifi ‘ya’ya huɗu.
Karon farko da wata damisa ta haifi ‘ya’ya hudu a Indiya, kamar yadda ministan muhallin ƙasar Bhupendar Yadav ya bayana.
Mista Yadav – wanda ya wallafa hotunan ‘ya’yan damisar a shafinsa na twitter – ya bayyana lamarin a matsayin wani abu na tarihi a harkokin gandun dajin ƙasar.