fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Kasar italiya bazata je gasar cin kofin Duniya ba a karin farko cikin shekaru sittin

Kasar Italiya bazata je gasar cin kofin kwallon Duniya ba da za’a buga a kasar Rasha idan Allah ya kaimu shekara me zuwa, hakan kuwa ya farune dalilin rashin nasarar da tayi a wasan da suka buga ita da Sweden jiya, wanda suka tashi babu wanda ya zura wa wani kwallo a raga.

Sweeden din dai tayi nasara akan Italy ne da kwallo daya data zurata mata a raga a wasansu na farko.

Wannanne karo na biyu a tarihin kasar Italiya sannan kuma na farko a cikin shekaru sittin da suka gabata (watau tun shekarar 1958) da bata samu zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya ba.

Karanta wannan  Bidiyo; Ni dai nasan wuta zan shiga dan bana aiki irin na 'yan Al-Aljannah>>Inji Wannan Tsohon

Italiya dai ta taba lashe kofin Duniya har sau hudu a tarihi kuma wasu na ganin rashin ta a gasar cin kofin Duniyar badi, watakila ya ragewa gasar armashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.