fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kasar Italiya ta killace mutane sama da Miliyan 15 saboda Coronavirus

Gwamnatin Italiya ta dauki matakin killace kashi 1 bisa 4 na daukacin al’ummar kasar, bayanda a safiyar yau ta dakatar da shige da fice a yankin arewacin kasar, don dakile yaduwar annobar murar Coronavirus dake barna a kasar.

 

Matakin killace arewacin kasar ta Italiya da ya shafi sama da mutane miliyan 15, zai ci gaba da wanzuwa har ranar 3 ga watan Afrilun dake tafe, inda dole sai da kwakkwaran dalili za a baiwa mutane damar shiga yankin arewacin Italiyan, ciki har da biranen Venice da Milan.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

 

A wani matakin kuma gwamnatin Italiyan ta rufe baki dayan gidajen Sinima, filayen wasannin kalankuwa da kuma gidajen adana kayan tarihi dake kasar, duk dai kan annobar murar ta Coronavirus.

 

Jami’an lafiya sun ce yanzu haka annobar ta Coronavirus ta halaka mutane sama da 200, kusan dubu 6 kuma sun kamu a kasar ta Italiya.

RFIhausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.