Jiya ranar sati 16 ga watan mayu aka cigaba da buga wasannin gasar Bundesliga tare da bin dokokin da aka tsara masu. Suma hukumar Premier League suna shirin cigaba da wasannin nasu a watan yuni, amma sai dai suna cecekuce akan buga wasannin ba tare da yan kallo ba.
Duk da cewa kasar jamus ta sassauta dokar zaman gida ranar juma’a kuma taba masu gidajen cin abinci da sauran su damar cigaba da ayyukan su, an cigaba da buga wasan kwallon kafa ba kusan tare da yan kallo ba.
Saboda mutane guda 300 ne kacal aka bari suka shiga filin wasan, kuma kafin su shiga sai da suka rufe fuskokin su kuma aka auna zafin jikin su.