fbpx
Friday, May 27
Shadow

Kasar Saudiyya ta fara baiwa harkar nishadi muhimmanci: An shirya taron masu baiwa mutane Dariya: Mace tayi waka a gaban mutane

A satin daya gabatane aka ga wani abu da ba’a saba ganin irinshi ba a kasar Saudiyya, domin kuwa hukumomin kasarne suka shirya wani taron nishadi wanda aka tara masu ba bayar da dariya da kuma mawaka, ciki hadda mata suka nishadantar da mutane, wannan abun ya baiwa Duniya mamaki, domin kuwa a baya ansan kasar da kiyaye irin wadannan abubuwan na nishadi da waka da kuma tara maza da mata a guri daya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Amma a wannan taron da akayi mata da maza sun zauna a guri daya, duk da yake cewa wadanda sukayi wasannin barkwanci na baiwa mutane dariya duk mazane, amma an samu mace daya tayi waka a gurin, kuma masu shiya wannan shagali sun bayyana cewa, wanda za’ayi shekara me zuwa zai kunshi mata, masu wasannin ko kuma bayar da labarin bayar da dariyar.

Wannan dai yana cikin wani sabon tsari da yariman kasar ta Saudiyya me jiran gado, Muhammad Bin Sulaiman ya fito dashi wanda yace zai kawar da masu tsatstsauran ra’ayin addinin islama, ayi tsarin musulunci wanda ke da sauki akan abubuwan rayuwa.

A cikin sabon tsarin dai akwai baiwa mata damar damar yin tuki da kuma bude gidajen kallo na silm, wadanda tuni sun dade a kulle an haramta amfani dasu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tsohon Hoton Farfesa Osinbajo da iyayensa lokacin da ya gama makaranta

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.