
Tau masu burin zuwa Saudiyya su dauki hotuna musamman a cikin masallatan, Harami da masallacin Annabi(S.A.W) sai su canja tunani domin kuwa kasar ta saudiyya ta hana daukar hotuna a cikin masallatan guda biyu a cikin wata sanarwa data fitar yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Sanarwar wadda Daractan kula da harkar watsa labarai da ‘yan jarida na kasar ta sadiyya ya fitar yace ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje na kasarne suka fitar da ita domin kare masallatan guda biyu da kuma ayyukan Ibada da mutane suka aikatawa a ciki.
Sanarwar tace irin masu daukar hotunan suna takurawa masu ayyukan Ibada, kuma anaso a killace masallcin daga abubuwan da basu dace ba, hakan na daga cikin dalilan da suka sa aka dauki wannan mataki.
Haka kuma koda ‘yan jaridane ba’a yadda su dauki hoto ko wane irine ba ko kuma na bidiyo a ciki ko kuma harabar masallacin ba, sanarwar ta bayyana cewa idan aka samu wani ya karya wannan doka to hukuma zata kwace abinda yayi amfani dashi din wajan daukar hoton.
A farkon wannan satin da muke cikine aka samu wani bayahude dan kasar Isra’ila ya dauki hoto a masallacin Annabi, inda ba’a yadda wanda ba musulmi ba ya shiga, hakan ya jawo hatsaniya da ruwan Allah wadai musamman a dandalin sada zumunta na kasar ta Saudiyya.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});